Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kwamitin ya kara da cewa mutum na biyar da aka kashe ya mutu sanadiyyar raunukan day a samu ne bayan da ya gwangwanin hayaki mai sa hawaye ya same a kirjinsa lokacin da jami’an tsaro ke murkushe masu zanga-zangar a ranar Alhamis.
Zanga-zangar dai ita ce zagaye na goma sha daya na gagarumin gangamin da jerin gwanon da ke gudana tun bayan juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktoba da ya yi sanadiyar hambarar da firaminista Abdalla Hamdok kafin a maido da shi.
Kwamitin likitocin Sudan ya ce adadin mutanen da aka kashe tun lokacin da jami'an tsaro suka fara murkushe wannan yunkuri daga ranar 25 ga watan Oktoba zuwa yanzu ya kai 53.
Masu zanga-zangar dai na neman cewa sojojin kasar su koma bariki kawai domin kuwa ba su da wata rawar da za su taka a sha’anin tafiyar da gwamnatin kasar a lokacin wa'adin rikon kwarya da zai kare , tare da neman a gudanar da zabe cikin 'yanci.
A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar jiya Juma’a ta ce an kashe mutane hudu a Omdurman, yayin da masu zanga-zangar 297 da kuma jami’an ‘yan sanda 49 suka samu raunuka a zanga-zangar adawa da mulkin soja a ranar Alhamis da ta gabata, inda dubun dubatar mutane suka shiga gangamin.
342/